Ajiyar Sani Abacha: Gwamnatin tarayya na dab da samun $500M daga kasar US, Uk da France

Gwamnati tarayya ta sanar cewa tana dab da samun wasu kudade daga kasar Amurka, Ingila da Faransa wanda tsohon shugaban kasa ya kai ajiya

Gwamnatin tarayya na dab da samun dala miliyan 500 daga cikin kudin da tsohon shugaban kasa, Sani Abacha ya kai ajiya kasar France da Ingila da Amurka.

Alkalin alkalan Nijeriya kuma ministan sharia, Abubakar malami, ya bayyana hakana bayan zaman majalisa da suka yi ranar laraba 13 ga watan Yuni.

Kamar yadda ya bayyana, gwamnatin Nijeriya tana tattaunawa da kasashen domin samun kudaden.

Labarin ya biyo bayan sanarwa da ministan kudi, Kemi Adeosun, tayi na cewa an tura dala miliyan $322,515,931.83 daga kasar Switzerland zuwa asusun babban bankin kasa na daga cikin kudin da Abacha ya wawure.

Abubakar Malami ya kara da cewa an mika takardar shaidar mayara da kudin da aka samo ga sauran yan majalisa.

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *